Amfara tattara sakamakon zaɓen jihar Edo
Tun ƙarfe 2:30 na rana kusan duka rufunan zaɓen da ke ƙananan hukumomi 18 na Edo suka rufe tantance masu zaɓe inda kuma wasu a lokacin suka fara ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa.
Sai dai akwai wasu rumfunan zaɓen kayayyakin zaɓe ba su isa da wuri ba, wanda hakan ya sa ba su fara zaɓe da wuri ba.
Tuni wasu rumfunan zaɓen suka ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa, inda Jam'iyyu biyu da suka fi shahara na APC da PDP ke nasara.
A yanzu dai an fara kai akwatuna gAmfara tattara sakamakon zaɓen jihar Edoundumomi inda ake tattara alƙaluman zaɓe.
Gwamnan jihar Godwin Obaseki ne ke takara ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, sai kuma Fasto Osagie Ize-Iyamu ƙarƙashin Jam'iyyar APC.
Sakamakon farko-farko da ya fara fitowa ya nuna duka 'yan takarar sun lashe rumfunan zaɓensu.
Comments
Post a Comment