Ƴan daban PDP na barazana ga zaɓen jihar Edo- APC
Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta yi ikirarin cewa 'yan daba da ke yi wa jam'iyyar PDP aiki suna zuwa rumfunan zabe da ake tunanin APC za ta samu rinjaye sun fatattakar masu zabe da ma'aikatan INEC.
A sanarwar da Kakakin yakin neman zaben gwamnan Edo na APC John Maiyaki ya fitar, ya lissafa wasu rumfunan zabe da ya yi ikirarin 'yan daban sun tafi sun tarwatsa masu zabe.
Comments
Post a Comment