MINISTAN JINƘAI TAYI AUREN SIRRI

 Tun bayan da labarin ya fara yaɗuwa kan batun auren Ministar Jin-ƙai da kare Afkuwar Bala'i ta gwamnatin Najeriya Hajiya Sadiya Farouq da shugaban rundunar sojin saman ƙasar Sadiq Baba Abubakar, mutane da dama suka fara neman sanin gaskiyar labarin.

Binciken da BBC ta yi ta hanyar tuntuɓar wasu makusantan mutanen biyu ya tabbatar da cewa lamarin ya faru, kuma an ɗaura auren ne tun a Juma'ar makon da ya gabata.

Majiyoyin masu ƙarfi ta ɓangaren Minista Sadiya da Air Marshal Sadiq da suka buƙaci a ɓoye sunayensu sun ce an ɗaura auren ne cikin sirri a Abuja babban birnin ƙasar.

Sai dai ƴan Najeriya da dama na mamakin yadda za a ɗaura auren fitattun mutane irin waɗannan amma ba a bayyana lamarin ba, musamman ganin cewa aure abin alkhairi nMinistan jinƙai Sa'adiyya tayi Auren sirri ba abin ɓoyewa ba.

Amma ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce, ''ai babu inda aka ce dole sai mutum ya bayyana aurensa, idan dai an cika sharuɗɗan auren yadda ya kamata bisa tsarin Musulunci ai shi kenan an samu abin da ake so.''

Wata majiyar kuma ta daban cewa ta yi ''ba a bayyana auren ba ne saboda yanayin da ake ciki na ƙoƙarin taƙaita yaɗuwar cutar korona da bin ƙa'idon da gwamnati ta gindaya.''

A bara ne Najeriya ta ɗauki ɗumi bayan da wani labari ya yaɗu kamar wutar daji da ke cewa ministar ta auri Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar.

Sai dai daga baya ya bayyana cewa labarin ƙarya ne.

Dama sun daɗe tare ne?

Sadiya Farouq da Sadiq Abubakar

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama ke yi a shafukan sada zumunta na ƙasar.

An yi ta yaɗa wasu hotana da ma'auratan biyu suka ɗauka tare yayin wata ziyara da Air Marshal Saidq ya kai ofishinta, wanda Hajiya Sadiya ta wallafa a shafinta na Tuwita tun a watan Maris, ana tattauna batun auren da su.

Sai dai hakan bai isa hujja ta cewa ko a lokacin suna tare a matsayin masoyan juna ba.

Amma binciken da BBC ta yi daga waɗannan makunsantan ma'auratan ya tabbatar da cewa 'sun ɗan jima tare, sai dai auren ne Allah bai kawo lokacinsa ba sai yanzu,'' a cewarsu.

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Kafar yaɗa labarai ta PR Nigeria ma a nata rahoton ta tabbatar da cewa ta tattauna da wani malamin addinin Musulunci da ya shaida ɗaurin auren, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, inda ya ce ''shi aure a Musulunce ba dole sai ma'auratan sun halarci taron ɗaura shi ba, waliyyansu kaɗai sun wadatar".

''Ɗaurin auren ya samu halartar shaidu da kuma waliyyan ango da na amarya, da biyan sadaki da karatun Al-ƙur'ani. Kuma waɗannan su ne abin da aka fi so a samu a wajen ɗaura aure,'' a cewar malamin.

Wannan layi ne

Fatan alheri

Sadiya Farouq Facebook

Ƴan Najeriya da dama sun yi ta yi wa Hajiya Sadiya da Air Marshal Sadiq fatan alheri kan wannan aure nasu musamman a shafukan sada zumunta.

Da yawa addu'o'in zaman lafiya da samun zuri'a ta gari suka dinga yi musu.

Wannan layi ne

Wace ce Sadiya Farouq?

Sadiya Farouq ta kasance wacce aka fi yawan magana a kanta cikin ministocin Buhari.

Kafin ba ta mukamin Ministar Kula da Ayyukan Jinkai da Kare Afkuwar Bala'i da Ci-gaban Al'umma, Sadiya Farouk ce shugabar Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira da 'yan ci rani da wadanda rikici ya raba da muhallansu.

Don haka, ana iya cewa ta dade tana aiki da masu karamin karfi da gajiyayyu.

Sadiya Umar Farouk ta taba yin Jami'ar Kula da ke Asusun Jami'iyyar APC ta kasa daga watan Yunin 2013 zuwa watan Yunin 2014.

Daga nan ne kuma ta zama mamba ta majalisar kamfe din shugaban kasa a jam'iyyar ta APC, inda ta rike mukamin shugabar kwamitin tsarawa da sa ido da kaiwa-da komowa da samar da kudi.

Sadiya Farouk ta jagoranci tawagar da ta shirya zaben 2015 a jam'iyyar APC wadda kuma ta yi nasara.

Sadiya Farouq

Tsakanin shekarar 2011 da 2013, Sadiya Farouk ta rike mukamin Mai Kula da Asusun Jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC), jam'iyyar da Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2011

Jam'iyyar CPC na daya daga cikin jam'iyyu hudu a Najeriya da suka hadu suka kafa jam'iyyar APC a shekarar 2013.

Sadiya Umar Farouk 'yar asalin karamar hukumar Zurmi ce a jihar Zamfara kuma tana da digirin farko a bangaren Kasuwanci sannan digirinta na biyu a bangaren Diflomasiyya.

Ita ce mafi karancin shekaru a ministocin Shugaba Muhammadu Buhari inda take da shekara 45 da haihuwa.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

𝐍𝐈𝐆𝐄𝐑𝐈𝐀 @60:𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈𝐍 𝐒𝐎𝐉𝐀 𝐌𝐀𝐒𝐔 𝐇𝐀𝐋𝐈𝐍 𝐓𝐒𝐈𝐘𝐀 𝐃𝐀 𝐍𝐀 𝐊𝐈𝐑𝐊𝐈

𝙔𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙢𝙖𝙯𝙖𝙣𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙚 𝙩𝙨𝙞𝙣𝙩𝙖𝙧 𝙠𝙬𝙖𝙧𝙤𝙧𝙤𝙣 𝙧𝙤𝙗𝙖 𝙨𝙪𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙮𝙚𝙧𝙬𝙖 𝙟𝙖𝙢𝙖 𝙖