๐๐ฐ๐๐ฆ๐ง๐๐ญ๐ข๐ง ๐ค๐๐ง๐จ ๐ง๐ ๐ฌ๐จ๐ง ๐ค๐๐ฆ๐ ๐ฆ๐๐ญ๐๐ซ ๐๐ฌ๐ฆ๐๐ง ๐๐ฎ๐ ๐๐ฃ๐
๐๐ง๐ ๐ฒ๐ฎ๐ง๐ค๐ฎ๐ซ๐ข๐ง ๐ค๐๐ฆ๐ ๐ฆ๐๐ญ๐๐ซ ๐๐ ๐๐ฌ๐ฆ๐๐ง ๐๐ฎ๐ ๐๐ฃ๐ ๐๐ค๐๐ง ๐ ๐ฐ๐๐ฆ๐ง๐๐ญ๐ข๐ง ๐ค๐๐ง๐จ.๐๐ฎ๐ง๐ค๐ฎ๐ซ๐ข๐ง ๐ค๐๐ฆ๐ ๐ฆ๐๐ญ๐๐ซ ๐๐ซ ๐๐ฌ๐ฆ๐๐ง ๐๐ฎ๐ ๐๐ฃ๐
Barista Sa'ida Sa'ad, matar fitatcen ษan siyasar nan Dr. Usman Bugaje na
fuskantar barazanar kamu daga wasu da ake zargin jami'an tsaron 'yansanda ne daga Kano.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa ana neman kama Sa'ida ne bisa zargin caccakar gwamnan Kano, akan yadda ta ce ya ษarnatar da tallafin Covid 19.
'Yansandan sun je har garin Kaduna a ฦoฦarisu na kama Barista Sa'ida, wacce take 'yar rajin kare haฦฦin ce a gidan aurenta, bisa zargin ษata suna.
A faifan murya da Baristan ta saki, ta yi zargin gwamnan na ฦoฦarin arzuta kan shi da kuษin tallafin korona.
A halin da ake ciki, ฦungiyoyin sa kai da kare haฦฦoฦin al'umma guda 49 ne suka rattaba hannu a wata takardar ฦorafi tare da kiran jami'an tsaron da su janye daga yunฦurin da suke na kame Baristar.
ฦungiyoyin sun ce. "A ranar Laraba 16/9/2020, da misalin ฦarfe 5 na yamma, wasu gungun mutane maza da mata suka faษo gidan Barista Sa'ida Sa'ad dake Kaduna cikin fararen kaya, inda suka yi yunฦurin kamata a zuwan su 'yansanda ne daga Kano, da aka turo su tafi da ita can Kano, don tuhuma da amsa wasu tambayoyi bisa zargin ษata sunan gwamnan Kano."
Sun ฦara da cewa. "Sun zo a motar bas mara tambari da Honda kalar azurfa, inda suka samu jagoranci wata ASP Zainab. Bisa la'akari da matsalar satar mutane da ake fama a ฦasar da kasancewar ba sa ษauke da takardar sammace, ta ฦi yarda ta fito daga gida, wanda a ฦarshe dole suka tafi.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa mutanen sun sake komawa a ranar Juma'a da misalin ฦarfe 1:15 na rana, ษauke da takardar sammace.
Jami'an tsaron sun kutsa kansu cikin gidanta, inda suka dinga yi wa ma'aikatan gidan barzana tare da daukar hotunan lambobin motocin dake gidan.
A ฦarshe sun nemi Sa'ida sama ko ฦasa, babu ita a gidan, hakan ya tilasta a wannan karon ma sai tafiya suka yi.
ฦungiyoyin sun bayyana a shirye Barista Sa'ida take ta amsa sammacen, matuฦar an bi ฦa'idar da ta kamata.
Comments
Post a Comment