RUWAN SAMA KAMAR DA BAKIN KWARYA YA KASHE WUTAR DAJI DA TA KWANA GOMA TANA CI
Ruwan Sama Ya Kashe Wutar Daji Bayan kwashe kwanaki 10 tana ci a dajin Australia. Daga Wakilinmu. Tsawon wasu kwanakin da wata mummunar Gobara tayi tana ci a Kasar Australia wadda ta yi barna mai yawan gaske,daga karshe dai Allah cikin tausayinsa da jinkansa ya kawo masu daukin mutuwar gobarar ta hanyar wani gilgijen da yazo ya saukar da ruwa a daidai yankin da gobarar ke ci. Kafin nan,duk Kokarin da 'yan kwana-kwana (Masu kashe gobara) ke yi na ganin Mutuwar wannan gobara da a iya cewa wani Ibtila'i ne daga Ubangiji tsawon wadannan kwanaki amma abin sai ma kara kambama yake yi har sai da Allah ya kawo iyakarsa a jiya Lahadi. Bayan safkar ruwan saman, wutar ta Mutu murus a yayin da kowa hankalinsa ya dawo a jikinshi cike da farin ciki da murna.Abin mamaki hatta Dabbobi,ka iya cewa su ma suna murna ta hanyar yadda suke walwala da tsalle ya junansu. Gobarar dai ta ja asarar Mutuwar Dabbobin Daji da wuraren Kiwon Dabbobi,bayan Asarar dukiya har ma da ta rayukan Mutane. ...