Posts

'YAN SHI'A A NAJERIYA SUN GUDANAR DA TATTAKI

Image
'Yan shi'a sungudanar da Tattaki a Najeriya. Kamar ko wace shekara 'yan shi'a mabiya El'zakzaky a Najery suna gudanar da Tattaki domin kwatanta irin abinda ya faru ga jikan Annabi (S) sayyadi Husain. 'Yan shi'ar sunbi sahun takwarorin su na sassan duniya da suke takawa a kasa zuwa birnin karbala domin ziyarar sayyadina Husain.  A Najeriya 'yan shi'ar suna tashi ne daga bangarori shida zuwa Zariya su karkare tattakin nasu a can kuma suyi addu'a da jawabi daga bakin Sheikh El'zakzaky. Amma tun bayan arangama da aka samu tsakanin su, da sojoji a shekarar 2015 wanda yayi sanadiyyar mabiya malamin 347 a rahoton gwamnatin, da jikkata wasu da dama, gami da kama Sheik El'zakzaky da matarsa, yasa suka janye da zuwa cikin Birnin na Zariya domin kaucewa wata matsalar. Duk da haka a wasu lokutta ana samun kashe kashe daga jami'an tsaro abisa hanyar tasu kafin zuwa inda zasu karkare tattakin kamar a kano da aka taba samun asarar rayuka da dama, sh...

ƘASAR MASAR TA GANO AKWATIN GAWA DA AKA BINNE TSAWON SHEKARA 2,500

Image
   Masar ta gano akwatinan gawa da aka binne shekara 2,500 AFP Copyright: AFP Masana tarihi a Masar sun ce sun gano akwatunan gawa 59 da aka binne cikin yanayi mai kyau, a makonnin baya-bayan nan. Kamfanin dillacin labarai na AFPya ruwaito cewa daya daga cikin akwatunan da aka bude wanda ya kwashen sama da shekara 2,500 a kasa, masana tarihin sun ce an naɗe wanda ke ciki ne da farin tufafi. Tun bayan gano wasu akwatina 13 da aka yi sati uku baya, ake ci gaba da gano wasu masu yawa a haƙar da ake yi wadda ba ta wuce mita 12 be, kwatankwacin taku 40. AFP Copyright: AFP Za a iya gano wasu akwatunan a binne a ƙasa, in ji ministan kula da harkokin yawon buɗe ido Khaled al-Anani, wanda ya bayyana hakan a kusa da pyramid of Djoser da ya kusa shekara 4,700. Haƙar da ake yi a Saqqara a yan shekarun nan, takai ga samo wasu abubuwa da mutanen baya suka kera da kuma gawawwakin dabbobi irin su maciji tsintsaye da kwari da dai wasu sauran dabbobi. AFP Copyright: AFP Article share tools  View m...

MUHIMMAN ABUBUWA BIYAR DA BUHARI YAYI MAGANA A KANSU-bbc hausa

Image
Nigeria @60: Muhimman abubuwa biyar da Buhari ya ce yayin jawabinsa Sa'o'i 5 da suka wuce ASALIN HOTON, NIGERIA PRESIDENCY A ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoban 2020 ne Najeriya ta cika shekara 60 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka. A safiyar Alhamis ne shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi jawabi na musamman ga 'yan ƙasar inda jawabin ya fi mayar da hankali kan haɗin kan ƙasar. Ga wasu daga cikin muhimman batutuwan da shugaban ya taɓo a jawabinsa: Haɗin kai Jigo ko kuma babban saƙo a cikin jawabin shugaban ƙasar shi ne kan batun haɗin kai, domin shugaban a wurare daban-daban ya nuna cewa idan 'yan ƙasar suka haɗa kansu za a samu ci gaba mai ɗorewa. "Idan muka haɗa kanmu za mu iya sauya yadda muke a yanzu domin kawo ci gaba mai amfani a garemu kuma za mu iya taimakon kanmu ƙwarai". Shugaba Buhari ya bayyana cewa ta hanyar haɗin kai ne 'yan Najeriya za su magance ƙalubale daban-daban da suke fuskanta Warkar da Najeriya daga raunin da ta samu...

𝐒𝐢𝐲𝐚𝐬𝐚𝐫 𝐚𝐬𝐚𝐥𝐢𝐧 𝐁𝐚𝐡𝐚𝐮𝐬𝐡𝐞 𝐛𝐚𝐦𝐚𝐠𝐮𝐣𝐞

Image
 𝐒𝐢𝐲𝐚𝐬𝐚𝐫 𝐚𝐬𝐚𝐥𝐢𝐧 𝐁𝐚𝐡𝐚𝐮𝐬𝐡𝐞 𝐁𝐚𝐦𝐚𝐠𝐮𝐣𝐞:ℎ𝑟𝑡𝑣𝑛𝑒𝑡𝑤𝑜𝑟𝑘.𝑛𝑔@𝑔𝑚𝑎𝑖𝑙.𝑐𝑜𝑚 𝐷𝑜𝑚𝑖𝑛 𝑎𝑖𝑘𝑜 𝑚𝑎𝑛𝑎 𝑑𝑎 𝑠ℎ𝑎𝑤𝑎𝑟𝑎 𝑘𝑜 𝑟𝑎ℎ𝑜𝑡𝑎𝑛𝑛𝑖. Wata shekara, aiki ya kaini wata jiha a cikin jihohin arewa maso gabas. Da yamma sai na fito daga otel ɗin da aka yi mana masauki, da nufin zagawa inga gari. Ko ba komi, ai Hausawa sun ce na zaune bai ga gari ba. A cikin gari nayi isha'i, sa'annan na fara tattaki da nufin dawowa masauki. A bisa hanya na hango wani shagon abinci irin wanda Turawa ke kira restaurant. Sai na faɗa da nufin yin ƙoto. Bayan na zauna, an kawo mani irin abincin da na buƙata har na fara ci, sa'annan ne na ankara da hirar da wasu matasa suke yi a wani teburin da ke cikin ɗakin abincin. Matashi na Farko: Kakana, wanda ya daɗe a cikin hausawa, shine ya ke tabbatar mani da cewa babu wasu mutane da ake kira hausawa. Duk wanda kaji ance bahaushe ne, to in ka bincika yana da asali a wata ƙabilar cikin kakanninsa. Matashi na Biyu:...

MAZAUNA KANO SUN KOKA BISA YAWAITAR SACE-SACEN GARIN TUWO

Image
   M  azauna Kano Sun Koka Bisa Yawaitar Sace-Sacen Garin Tuwo a Wajen Mas Mazauna Unguwannin Kurna, Dandishe da  Gobirawa dake Karamar hukumar Dala ta jihar Kano sun koka bisa yawaitar satar garin tuwo a wajen masu nika a jihar. Jaridar PRIME TIME NEWS ta rawaito cewa mazauna unguwannin sun yi korafin yawan bacewar gari a wajen nika a yan kwanakin nan, wanda hakan ya haifar da damuwa tsakanin mutane, musamman ganin yadda tattalin arzikin kasarnan ke cikin mawuyacin hali.  Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa yawancin wadanda lamarin ya shafa, masu karamin karfi ne wadanda baza su iya siyan shinkafa ba sai dai su ci abin da ya shafi gari musamman masara da gero, wanda dole ne a nika shi kafin a sarrafa shi. Haka kuma, wannan jaridar ta gano cewa mazauna wasu yankuna a kwaryar birnin jihar Kano a yan kwanakin nan suna fuskantar yawan satar Gari a wajen masu nika, wanda hakan ya tilasta musu kula da abincin na su. Mamman Sani, wanda ke yin nika a Gobirawa, Kurna ya bayyana cewa...