Posts

Kasar Iran Za Ta Halba Wasu Taurarin Dan Adam Masu Nisan Kilomita 1000 Daga Doran Kasa.

Image
Iran Za Ta Harba Taurarin Dan Adam Tsawon Kilo Mita 1000 Daga Doron Kasa. Shugaban hukumar kula da ayyukan sararin samaniya na kasar Iran, Mortadha Barari ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu masu zuwa Iran za ta harba wasu taurarin dan adam zuwa sararin samaniya tsawon kilo mita 1000 daga doron kasa. A lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Tehran, Barari ya bayyana cewa, baya ga shirin da suke dashi na harba wasu taurarin dan adam a cikin wannan makon mai kamawa, suna da wani shirin na daban tsakanin shekara guda zuwa shekaru biyu masu zuwa. Ya bayyana cewa wannan yana daga cikin babban ci gaban da suka samu a bangaren ilimin kimiyya, wanda ya mayar da Iran din ta zama ta daya ayankin gabas ta tsakiya wajen harba tauraron dan adam, kamar yadda kuma ita ce ta tara a duniya a halin yanzu a wannan fage. Ya ce kammala aikin shekaru biyu masu zuwa, Iran din za ta harba wasu taurarin dan adam tsawon kilo mita dubu 36 daga doron kasa.

Gwamna Zulum ya nuna rashin sha'awarsa na wani ya yi masa tattakin karramawa.

Image
'Ka sha zamanka ka huta na gode da kauna'- Sakon Gwamna Zulum ga matashi da ya fara tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri. Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira ga matashi Usman Zubairu, wanda ya sanar da cewa zai yi tattaki daga jahar Jigawa zuwa Maiduguri domin jinjinawa gwamnan kan ayyukan da yake yi cewa yayi zamansa amma ya gode. Gwamnan ya bayyana hakan ne da yammacin Juma'a a shafinsa na Tuwita Yace: "A'a, Nagode, dan uwa Usman Zubairu." Ya kara da cewa; "Na samu wani labarin cewa wani matashin dan uwa Usman Zubairu, ya kaddamar da tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri domin karramani." Ya ci gaba da cewa "Ina mai matukar godiya Malam Usman bisa ga goyon bayarka amma ina rokonka ya ajiye wannan tafiya." "A nawa fahimtar, ya zo Maiduguri tuni. Ina kira garemu mu sanya jihar Borno da Najeriya cikin addu'o'inmu. Hakan ya fi kyau." Usman Zubairu dai ya bayyana cewa zai yi tattaki daga jihar...

Batanci Ga Alzakzaky Ya Ja Wa Wani Matashi Hukunci A Kotu.

Image
Wata Kotu ta daure wani Matashin akan ya yi 6atanci da Hoton Shaikh Alzakzaky. A ranar talatar na da ta gabata (4/2/2020) ne, wata Kotun Majistare da ke Potiskum jihar Yobe ta yanke wa wani matashi mai suna Mohamad Garba hukuncin daurin watanni shida a gidan kaso ko kuma tarar Naira dubu 10,000 a bisa samunsa da laifin 6ata sunan Malamin Addinin Musulunci shugaban 'yan uwa Musulmi a Najeriya, Shaikh Alzakzaky,ta hanyar amfani da Hoton Malamin a cikin wani bidiyon 6atanci da ya yi wa wasu Mata ya sakie shi a kafafen sadarwa. Bidiyon mai tsawon mintuna biyu da dakika 40 da Matashin ya saki kafafen sadarwa na zamani a ranar 26 ga Janairun 2020,ya nuna yadda yake 6atanci ga wasu matan da ba su da Hijabi a jikinsu yana kuma tallatasu da cewa "ana gwanjonsu",a inda daga karshen bidiyon ya dauka da Hoton Malam Alzakzaky, sakamakn haka Almajiran Malamin suka yi kararsa da sunan ya yi 6atanci da zub da Mutunci wa Malamin nasu. Almajiran Malamin sun binciko matashin sukakuma ...

Kotu Ta Ba Da Umurnin A Rika Barin Likitocin Alzakzaky Suna Ganawa Da A Duk Sadda Ya Bukaci Hakan.

Image
SHARI'AR SHEIKH ALZAKZAKY: Kotun Tarayya da ke Kaduna a zamanta na yau Alhamis domin ci gaba da sauraren Karar da gwamnatin Jahar ta shigar akan wasu tuhumce-tuhumce da ta ke yi wa Jagoran 'yan uwa Musulmi Shaikh Ibraheem Alzakzaky da mai dakinsa Malama Zeenatu,Kotun ta ba da umurnin a rika barin Likitocin Shehin Malamin su rika duba lafiyar sa a cikin gidan Yari a duk lokacin da suka bukaci haka. Shehin Malamin dai na ci gaba da tsarewa ne tun Watan Disambar 2015,biyo bayan kashe daruruwan Almajiransa, 'yayansa da wasu 'yan uwansa na jini a yayin da shi kansa da Matarsa ba su tsira daga halbin harsasan da Sojoji suka yi masu wanda har yau suke cikin rashin lafiya sakamakon illar da harsasan su kai masu a jiki. Za dai a ci gaba da sauraren karar ne a ranar 24 da 25 na watan da muke ciki,bayan rashin halartar Malamin da Matarsa a zaman Kotun na yau sakamakon rashin lafiyar da ke su fama da ita, kamar yadda Lauyan Malamin Femi Falana ya bayyana. Menene ra'ayinku...

"...DA SOJOJIN NAJERIYA MUKE YAKI" -ZULUM

Image
Babbar Magana: "Yanzu ba da kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram muke yaki ba, da sojojin Najeriya muke yaki. Domin yanzu sojoji suna aiki kafada da kafada da 'yan Boko Haram ne shi yasa matsalar rashin tsaro ke karuwa a Najeriya. Najeriya za ta yi nasara akan 'yan Boko Haram ne idan sojoji suna yakin 'yan Boko Haram da gaske." — Gov. Farfesa  Babagana Zulum https://www.youtube.com/channel/UCbyByJ3TbE5Q7Is_6tDHo_A

RUWAN SAMA KAMAR DA BAKIN KWARYA YA KASHE WUTAR DAJI DA TA KWANA GOMA TANA CI

Image
Ruwan Sama Ya Kashe Wutar Daji Bayan kwashe kwanaki 10 tana ci a dajin Australia. Daga Wakilinmu. Tsawon wasu kwanakin da wata mummunar Gobara tayi tana ci a Kasar Australia wadda ta yi barna mai yawan gaske,daga karshe dai Allah cikin tausayinsa da jinkansa ya kawo masu daukin mutuwar gobarar ta hanyar wani gilgijen da yazo ya saukar da ruwa a daidai yankin da gobarar ke ci. Kafin nan,duk Kokarin da 'yan kwana-kwana (Masu kashe gobara) ke yi na ganin Mutuwar wannan gobara da a iya cewa wani Ibtila'i ne daga Ubangiji tsawon wadannan kwanaki amma abin sai ma kara kambama yake yi har sai da Allah ya kawo iyakarsa a jiya Lahadi. Bayan safkar ruwan saman, wutar ta Mutu murus a yayin da kowa hankalinsa ya dawo a jikinshi cike da farin ciki da murna.Abin mamaki hatta Dabbobi,ka iya cewa su ma suna murna ta hanyar yadda suke walwala da tsalle ya junansu. Gobarar dai ta ja asarar Mutuwar Dabbobin Daji da wuraren Kiwon Dabbobi,bayan Asarar dukiya har ma da ta rayukan Mutane. ...

RAHOTANNI DAGA BAGHADAD TA KASAR IRAQ

Rahotanni sun bayyana cewa;Jakadan Amurka ya tsere daga Bagagaza sakamakon boren Al'umma. Daga Awwal Isa Musa Bayan ayyana zaman makoki na kwana 3 wanda Firaministan riko na Iraqi Adel Abdul Mahdi yayi,da kuma furucin Allah wadai ga Amurka wanda babbabn marja'in Addini na Iraqi yayi ga Amurka,dubban mutane sun fito zanga-zangar la'anta da kin jinin Amurka a biranen Iraqi da dama. Mutanen da suka yi kwamba suka mamaye ofishin Jakadancin Amurka dake birnin Bagadaza,suna kiran "mutuwa ga Amurka!mutuwa ga Israila!sannan suna kiran da a kamo jakadan a hukunta shi.  Hakan ya tilasta tserewar Jakadar daga ofishinsa dake " Green Zone" zuwa wata mabuya ta daban,abin da har yanzu an ki a bayyana inda jakadan ya buya. An bayyana cewar,an ga wasu da boyayyun fusaku cikin bakaken mota suna tserewa,daga nan aka sanar da ficewar jakadan. Masu zanga-zangar na kira da "Tilas a rufe ofishin jakadancin Amurka dake Baghdad, Iraqi,kuma tilas majilisar kasar tayi do...

DANGANTAKAR DAUKAR NAUYIN FILMS DA ISAR DA SAKO

Dangantakar Daukar Nauyin Shirya Fim Da Isar Sa'ko? A wannan zamani fim ya Zama tamkar Hantsi leka Gidan Kowa, da wuya ka sami wani mutum daya wanda bashi da alaka da fim ko da kuwa ta kallo ce. Wani sanannen abu kuma shi ne kadan ne daga cikin mutane masu kallon Fim suke da masaniya akan dalilin da yasa ake shirya fim har ya zo gare su su kalla. A fiye da shekaru 100 da suka gabata zuwa yau Fim ya shiga jerin Hanyoyin isar da sako mafi sauri da kuma saukin fahimta. Wannan dalilin yasa 'yan mulki mallaka suka rungumi wannan hanya ta fim wajen yada manufofinsu ga sauran Al'umma. Wasu al'ummun ba su yi fargar jaji ba sun lura da wuri irin barnar da Fim din Turawa ya soma haifarwa a cikin Al'ummar su musamman ga matasa, ganin haka sai suma suka soma shirya fim domin kare kai. Duk Wanda ya Kalli Fima-Fimai na Indiya a Farkon al'amarin Fim din su zaka ga ba komai a ciki sai yada al'adunsu,  sun yi hakan ne kuwa domin mayar da martani ga harin da 'yan mu...

YANDA AKE RUBUTA LABARI

What Exactly Is a Script? What Exactly Is a Script?  A script is a document that outlines every aural, visual, behavioral, and lingual element required to tell a story. Why "outlines"? Because film is a highly collaborative medium and the director, cast, editor, and production crew will, based on your "outline", interpret your story their way when it is filmed. They may consult you, or they may not. Other writers may be brought in or you may be asked to re-write the entire thing. That's life, in the world of screenwriting. But because so many people are involved in the making of a film, a script must conform to standards that all involved parties understand and thus has a specific format or layout, margins, notation, and other conventions. This document is intended to overview the typical elements used screenplay writing.  It is crucial to remember that film is a VISUAL medium. You don't tell your audience your story, you SHOW them. You must learn to write a...
Image
HRTV DOMIN AL'UMMA            08036342932 Kukasan ce tare da HRtv network domin samun sababbin shirye shirye masu fadakarwa da ilimantarwa gami da nishadi Somin tabi kushiga nan domin kuganema idonku  https://youtu.be/2AoOkmms_To By mziag
Image
HRTVnetwork wan'nan shafi da aka kirkira ankirkireshi ne domin Al'umma.  Zai dunga kawomaku labaru na gida Nigeria da na kasashen waje.  Kudai ku kasance da HAUSAWA RADIO AND TELEVISION network 'yancin fadin ra'ayi. 08036342932