Posts

๐†๐ฐ๐š๐ฆ๐ง๐š๐ญ๐ข๐ง ๐ค๐š๐ง๐จ ๐ง๐š ๐ฌ๐จ๐ง ๐ค๐š๐ฆ๐š ๐ฆ๐š๐ญ๐š๐ซ ๐”๐ฌ๐ฆ๐š๐ง ๐›๐ฎ๐ ๐š๐ฃ๐ž

Image
 ๐€๐ง๐š ๐ฒ๐ฎ๐ง๐ค๐ฎ๐ซ๐ข๐ง ๐ค๐š๐ฆ๐š ๐ฆ๐š๐ญ๐š๐ซ ๐ƒ๐Š ๐”๐ฌ๐ฆ๐š๐ง ๐๐ฎ๐ ๐š๐ฃ๐ž ๐š๐ค๐š๐ง ๐ ๐ฐ๐š๐ฆ๐ง๐š๐ญ๐ข๐ง ๐ค๐š๐ง๐จ. ๐˜๐ฎ๐ง๐ค๐ฎ๐ซ๐ข๐ง ๐ค๐š๐ฆ๐š ๐ฆ๐š๐ญ๐š๐ซ ๐ƒ๐ซ ๐”๐ฌ๐ฆ๐š๐ง ๐๐ฎ๐ ๐š๐ฃ๐ž Barista Sa'ida Sa'ad, matar fitatcen ษ—an siyasar nan Dr. Usman Bugaje na  fuskantar barazanar kamu daga wasu da ake zargin jami'an tsaron 'yansanda ne daga Kano. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa ana neman kama Sa'ida ne bisa zargin caccakar gwamnan Kano, akan yadda ta ce ya ษ“arnatar da tallafin Covid 19. 'Yansandan sun je har garin Kaduna a ฦ™oฦ™arisu na kama Barista Sa'ida, wacce take 'yar rajin kare haฦ™ฦ™in ce a gidan aurenta, bisa zargin ษ“ata suna. A faifan murya da Baristan ta saki, ta yi zargin gwamnan na ฦ™oฦ™arin arzuta kan shi da kuษ—in tallafin korona. A halin da ake ciki, ฦ™ungiyoyin sa kai da kare haฦ™ฦ™oฦ™in al'umma guda 49 ne suka rattaba hannu a wata takardar ฦ™orafi tare da kiran jami'an tsaron da su janye daga yunฦ™urin da suke na kame Baristar. ฦ˜ungiyoyin sun c...

๏ผข๏ฝ•๏ฝˆ๏ฝ๏ฝ’๏ฝ‰ ๏ฝ™๏ฝ ๏ฝ‡๏ฝ๏ฝ“๏ฝ ๏ฝ‹๏ฝ—๏ฝ๏ฝ๏ฝ‰

Image
 BUHARI YA FASA KWAI - Karanta ka Raba a shafinka Dalilin da yasa Najeriya ta shiga cikin Matsalolin Tabarbarewar Tattalin Arziki da Talauci - Muhammadu  BUHARI ------------------------ Shugaba Muhammadu Buhari a birnin New York na kasar Amurka, ya sake yin bayani dalla - dalla kan dalilan da ya sa Nigeria ta samu kan ta cikin matsalolin da muke fama da su a yanzu. Shugaba Buhari yayi bayanin ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu 'yan Nigeria su 15 da suka yi fice tare da kwarewa a wuraren da suke aiki a kasar ta Amurka, wadanda Babbar Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Kasashen Waje, Mrs. Abike Dabiri-Erewa ta jagoranta suka gana da Shugaban Kasar. Ganawar ta bawa Shugaba Buhari damar yi musu bayanin dalla-dalla kan dalilan da ya sa 'yan Nigeria da kasar ke cikin wahalhalu a yanzun, sai dai ya basu tabbacin cewa idan dukkan 'yan Nigeria zasu bada gudunmawarsu ciki harda mazauna kasashen waje, Kasar za sake daidaituwa har ma a koma fiye da yadda ake a ...

๐™”๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™–๐™ฏ๐™–๐™ฃ๐™—๐™–๐™ฉ๐™– ๐™ ๐™š ๐™ฉ๐™จ๐™ž๐™ฃ๐™ฉ๐™–๐™ง ๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ง๐™ค๐™ง๐™ค๐™ฃ ๐™ง๐™ค๐™—๐™– ๐™จ๐™ช๐™ฃ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฎ๐™š๐™ง๐™ฌ๐™– ๐™Ÿ๐™–๐™ข๐™– ๐™–

Image
    An kama tsoffin kwaroron roba 320,000 da ake mayar wa sabbi Reuters Copyright: Reuters Ana wanke kwaroron ne a gyara sannan a sake mayar da su kamar sabbi a sayar. Image caption: Ana wanke kwaroron ne a gyara sannan a sake mayar da su kamar sabbi a sayar. ฦณan sanda a Vietnam sun ce sun kama kwaroron roba sama da 320,000 da aka yi amfani da su kuma ake sayar wa ba bisa ka’ida ba ga masu buฦ™ata. An nuna hotunan kwaroron da dama da nauyinsu ya kai 360kg a wani babban wurin ajiye kaya wanda a kwanan baya aka kai wa samame a kudancin lardin Binh Doung. An kama matar da ake tunanin ita ke da wurin ajiye kayan. Rahotanni sun ce ana wanke kwaroron ne a gyara sannan a sake mayar da su kamar sabbi a sayar. Matar ta ce akwai kuษ—i da ake biyanta kan ko wane kwaroron roba. Babu dai tabbaci kan yawan waษ—anda aka sayar a kasuwa. 

MINISTAN JINฦ˜AI TAYI AUREN SIRRI

Image
   Tun bayan da labarin ya fara yaษ—uwa kan batun auren Ministar Jin-ฦ™ai da kare Afkuwar Bala'i ta gwamnatin Najeriya Hajiya Sadiya Farouq da shugaban rundunar sojin saman ฦ™asar Sadiq Baba Abubakar, mutane da dama suka fara neman sanin gaskiyar labarin. Binciken da BBC ta yi ta hanyar tuntuษ“ar wasu makusantan mutanen biyu ya tabbatar da cewa lamarin ya faru, kuma an ษ—aura auren ne tun a Juma'ar makon da ya gabata. Majiyoyin masu ฦ™arfi ta ษ“angaren Minista Sadiya da Air Marshal Sadiq da suka buฦ™aci a ษ“oye sunayensu sun ce an ษ—aura auren ne cikin sirri a Abuja babban birnin ฦ™asar. Sai dai ฦดan Najeriya da dama na mamakin yadda za a ษ—aura auren fitattun mutane irin waษ—annan amma ba a bayyana lamarin ba, musamman ganin cewa aure abin alkhairi n Ministan jinฦ™ai Sa'adiyya tayi Auren sirri  ba abin ษ“oyewa ba. Amma ษ—aya daga cikin majiyoyin ya ce, ''ai babu inda aka ce dole sai mutum ya bayyana aurensa, idan dai an cika sharuษ—ษ—an auren yadda ya kamata bisa tsarin Musulunci ai...

Masarautar Zazzau- yarima Mannir ko Ahmad Bamalli?

Image
  Sarautar Zazzau: Makusancin Buhari, Yerima Mannir ne ko Amini kuma ฦŠan uwan El-Rufai, Ahmed Bamalli? Masarautar Zazzau, Aminin Buhari ko na El'rufa'i? Yanzu dai komai ya karkata zuwa Zariya domin can ne ake ta daka lissafe lissafen ko wa ye zai zama sabon sarkin Zazzau. Zuwa yanzu dai akwai alamar cewa Yeriman Zazzau Mannir Jaafaru wanda makusancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne na daga cikin wadanda ake ganin tabbas akwai yiwuwar ya zama sabon sarkin Zazzau. Mannir Jaafaru ษ—an tsohon sarki Jaafaru ฦŠan Isyaku ne wanda bayan ya rasu Sarki Aminu ya ษ—are kujerar sarautar Zazzau ษ—in, wato dai bai gaji mahaifin sa ba. A tsawon rayuwar sa Mannir ya fito ya nuna karara sarautar ce kawai a gaban sa, ya riฦ™a yi mata hidima ya na kai kansa ga ita sarautar ba da wasa ba. Wasu na ganin kusantar sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sa ya cimma burin sa na zama sarkin Zazzau. Sannan kuma sarakunan Arewa da dama shi suke so ayi wa sarkin na Zazzau. Magajin Gari Ahmed Bamalli Magajin...

Zaษ“en Edo: shin ankawo ฦ™arshen siyasar ubangida a Nigeriya?

Image
   Zaษ“en Edo: Shin an kawo ฦ™arshen siyasar ubangida a Naje  riya?   Nasarar da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya samu a zaษ“en da aka gudanar a ฦ™arshen mako ta bijiro da ayar tambaya: Shin an kawo ฦ™arshen siyasar ubangida a Najeriya? Wannan tambaya tana da matuฦ™ar muhimmanci ganin cewa an kwashe shekara da shekaru ana siyasar ubangida, wadda masana harkokin siyasa suke ganin ita ce take tarnaฦ™i game da gudanar da mulki na gari a ฦ™asar. Shi dai Mista Obaseki na jam'iyyar PDP, wanda Hukumar zaษ“en ฦ™asar ta INEC ta bayyana cewa ya samu ฦ™uri'u 307, 955, ya doke Mista Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC wanda ya samu ฦ™uri'u 223,619. Amma ba a nan batun siyasar ubangidan yake ba. An zaษ“i Gwamna Obaseki a matsayin gwamnan jihar ne a ฦ™arฦ™ashin jam'iyyar APC a 2016, kuma tsohon gwamnan jihar Adams Oshiomhole ne ya yi ruwa ya yi tsaki wajen gani nan zaษ“e shi. Sai dai wani rikici da ya ฦ™i ci ya ฦ™i cinyewa tsakanin Mr Oshiomhole, wanda tsohon shugaban jam'iyyar APC ne n...

Halin da ฦ™asa take ciki- wasu jigajigai a APC sun bada hakuri.

Image
  Wasu jigajigan jam'iyyar APC mai mulki sun fara neman afuwar jama'ar Nigeriya. Wasu jiga-jigan 'yan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun fara neman afuwar 'yan kasar a kan da su yi hakuri dangane da yanayin kunci da kasar take ciki yanzu haka sakamakon wasu matakai da gwamnatin kasar ke dauka da manufar gyara. Daya daga cikin jigo a jam'iyyar Farouk Adamu Aliyu, a cikin wata hira da ya yi da BBC, ya ce jama'a su yi hakuri da halin da ake ciki na matsi wanda ya ce dalilai ne suka haddasa hakan. Farouk Adamu Aliyu ya ce:"Ni ma a iya sanina ba na zaton an taba shiga kunci irin wannan na yanzu, kamar a bangaren abinci gaskiya ne an samu matsalar hauhawar farashi da dai sauransu". Ya ce abubuwa da dama ne suka kawo hakan, yana mai cewa mutane da dama sun sha kiransa ana yi masa Allah ya isa saboda yadda rayuwa ta yi kunci a yanzu. Jigo a jam'iyyar ta APC ya c:" Ga wadanda suke da-na- sanin tallafa mana da wani abu a lokacin da muke yakin ne...

Sarkin Zazzau ya rasu

Image
ASALIN HOTO Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris rasuwa. Ya rasu ranar Lahadi. Uban Garin Zazzau kuma Hakimin Soba, Alhaji Bashir Shehu Idris wanda ษ—a ne ga marigayin shi ne ya tabbatar wa da BBC labarin. Rahotanni sun ce Sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya ta mako biyu a wani asibiti da ke Kaduna. Za mu ci gaba da kawo muku ฦ™arin bayani. Tarihin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris Haihuwa da Tsatson Sarki Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris na shekarar 1936. Wanda ya haife shi ne Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi da ne, dan autan Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo. Shi kuma Sarki Muhamadu Sambo da ne, kuma na biyu a cikin 'ya'yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim. Shi kuma Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim shi ne na farko a daular Fulani karkashin jaddada addinin musulunci da Shehu Usumanu Danfodiyo y...

Zaษ“en jihar Edo: jam'iyyar APC tashiga farauta da gurgun kare.

Image
JAM'IYYAR APC TA SHIGA FARAUTA DA GURGUN KARE. Hukumar zaษ“e mai zaman kanta a Najeriya ta sanar da sakamakon zaษ“en gwamnan jihar Edo a ฦ™ananan hukumomi 13 daga cikin 18. Alkaluman da INEC ta fitar a hukumance sun nuna cewa Gwamna Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP ya bai wa babban abokin hamayyarsa Ize Iyamu na jam'iyyar APC tazara da dubban ฦ™uri’u. I zuwa ฦ™arfe tara na safiyar ranar Lahadi, hukumar INEC a cibiyar tattara sakamakon zaษ“e a Benin, babban birnin jihar Edo ta ce Obaseki na PDP ya samu ฦ™uri’u mafi rinjaye a ฦ™ananan hukuma 11 a yayin da Ize Iyamu ya lashe zaษ“e a ฦ™ananan hukumomi biyu. Ga sakamakon zaษ“en na ฦ™ananan hukumomin: Karamar Hukumar EGOR APC: 10202 PDP: 27621 Karamar Hukumar OWAN EAST APC: 19295 PDP:14762 Karamar Hukumar OVIA NORTH EAST APC: 9,907 PDP: 16,987 Karamar Hukumar ETSAKO WEST APC: 26,140 PDP: 17,959 Karamar Hukumar ESAN WEST APC: 7,189 PDP: 17,434 ฦ˜aramar Hukumar ESAN SOUTH EAST APC: 9237 PDP: 10563 ฦ˜aramar Hukumar OREDO APC: 18365 PDP: 43498 ฦ˜aramar ...