Iran Ta Yi Bikin Tunawa Da Zagayowar Ranar Samun 'Yancin Kai.
An Yi Bikin Tunawa Da Zagayowar Ranar Yuyin Juya-Hali Karo Na 41 A Kasar Iran. Daga Auwal Isa Musa. Magoya bayan kare Juyin-juya halin kasar Iran a jiya Talata,sun fito kwansu da kwalkwatansu domin jaddada mubayi'arsu ga tsarin da Kasar ke tafiya akanshi na Musulunci. Hakan na zuwa ne a lokacin da Kasar ta Iran ke bikin cika shekaru 41 cur da samun 'yancin kai na Juyin-juya hali daga Mulkin gurguzu zuwa na Musulunci da Malamin Addini Ayatollahi Ruhulla Alkhomaini ya Jagoranta a shekarar 1979. Duk ranar 11 ga Fabrelun kowace shekara dai, Al'ummar Kasar ta Iran na yin fitar farun-dango domin nuna farin cikinsu da yi wa juna barka gami da yin godiya ga Allah akan wannan sauyi da suka samu sama da shekaru 40,inda su kan gudanar da abubuwa daban-daban a matsayin shagulgula. Babban abin da Al'ummar kasar ke yi a wannan rana shi ne Muzaharori(demonstrations) a inda suke tafe suna rera wakokin Murna tare da daga Hotunan Jagoran wannan sauyin wato Ayatollah Alkhomaini,...