Posts

Masarautar Zazzau- yarima Mannir ko Ahmad Bamalli?

Image
  Sarautar Zazzau: Makusancin Buhari, Yerima Mannir ne ko Amini kuma Ɗan uwan El-Rufai, Ahmed Bamalli? Masarautar Zazzau, Aminin Buhari ko na El'rufa'i? Yanzu dai komai ya karkata zuwa Zariya domin can ne ake ta daka lissafe lissafen ko wa ye zai zama sabon sarkin Zazzau. Zuwa yanzu dai akwai alamar cewa Yeriman Zazzau Mannir Jaafaru wanda makusancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne na daga cikin wadanda ake ganin tabbas akwai yiwuwar ya zama sabon sarkin Zazzau. Mannir Jaafaru ɗan tsohon sarki Jaafaru Ɗan Isyaku ne wanda bayan ya rasu Sarki Aminu ya ɗare kujerar sarautar Zazzau ɗin, wato dai bai gaji mahaifin sa ba. A tsawon rayuwar sa Mannir ya fito ya nuna karara sarautar ce kawai a gaban sa, ya riƙa yi mata hidima ya na kai kansa ga ita sarautar ba da wasa ba. Wasu na ganin kusantar sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sa ya cimma burin sa na zama sarkin Zazzau. Sannan kuma sarakunan Arewa da dama shi suke so ayi wa sarkin na Zazzau. Magajin Gari Ahmed Bamalli Magajin...

Zaɓen Edo: shin ankawo ƙarshen siyasar ubangida a Nigeriya?

Image
   Zaɓen Edo: Shin an kawo ƙarshen siyasar ubangida a Naje  riya?   Nasarar da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya samu a zaɓen da aka gudanar a ƙarshen mako ta bijiro da ayar tambaya: Shin an kawo ƙarshen siyasar ubangida a Najeriya? Wannan tambaya tana da matuƙar muhimmanci ganin cewa an kwashe shekara da shekaru ana siyasar ubangida, wadda masana harkokin siyasa suke ganin ita ce take tarnaƙi game da gudanar da mulki na gari a ƙasar. Shi dai Mista Obaseki na jam'iyyar PDP, wanda Hukumar zaɓen ƙasar ta INEC ta bayyana cewa ya samu ƙuri'u 307, 955, ya doke Mista Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC wanda ya samu ƙuri'u 223,619. Amma ba a nan batun siyasar ubangidan yake ba. An zaɓi Gwamna Obaseki a matsayin gwamnan jihar ne a ƙarƙashin jam'iyyar APC a 2016, kuma tsohon gwamnan jihar Adams Oshiomhole ne ya yi ruwa ya yi tsaki wajen gani nan zaɓe shi. Sai dai wani rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin Mr Oshiomhole, wanda tsohon shugaban jam'iyyar APC ne n...

Halin da ƙasa take ciki- wasu jigajigai a APC sun bada hakuri.

Image
  Wasu jigajigan jam'iyyar APC mai mulki sun fara neman afuwar jama'ar Nigeriya. Wasu jiga-jigan 'yan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun fara neman afuwar 'yan kasar a kan da su yi hakuri dangane da yanayin kunci da kasar take ciki yanzu haka sakamakon wasu matakai da gwamnatin kasar ke dauka da manufar gyara. Daya daga cikin jigo a jam'iyyar Farouk Adamu Aliyu, a cikin wata hira da ya yi da BBC, ya ce jama'a su yi hakuri da halin da ake ciki na matsi wanda ya ce dalilai ne suka haddasa hakan. Farouk Adamu Aliyu ya ce:"Ni ma a iya sanina ba na zaton an taba shiga kunci irin wannan na yanzu, kamar a bangaren abinci gaskiya ne an samu matsalar hauhawar farashi da dai sauransu". Ya ce abubuwa da dama ne suka kawo hakan, yana mai cewa mutane da dama sun sha kiransa ana yi masa Allah ya isa saboda yadda rayuwa ta yi kunci a yanzu. Jigo a jam'iyyar ta APC ya c:" Ga wadanda suke da-na- sanin tallafa mana da wani abu a lokacin da muke yakin ne...

Sarkin Zazzau ya rasu

Image
ASALIN HOTO Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris rasuwa. Ya rasu ranar Lahadi. Uban Garin Zazzau kuma Hakimin Soba, Alhaji Bashir Shehu Idris wanda ɗa ne ga marigayin shi ne ya tabbatar wa da BBC labarin. Rahotanni sun ce Sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya ta mako biyu a wani asibiti da ke Kaduna. Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani. Tarihin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris Haihuwa da Tsatson Sarki Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris na shekarar 1936. Wanda ya haife shi ne Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi da ne, dan autan Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo. Shi kuma Sarki Muhamadu Sambo da ne, kuma na biyu a cikin 'ya'yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim. Shi kuma Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim shi ne na farko a daular Fulani karkashin jaddada addinin musulunci da Shehu Usumanu Danfodiyo y...

Zaɓen jihar Edo: jam'iyyar APC tashiga farauta da gurgun kare.

Image
JAM'IYYAR APC TA SHIGA FARAUTA DA GURGUN KARE. Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta sanar da sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo a ƙananan hukumomi 13 daga cikin 18. Alkaluman da INEC ta fitar a hukumance sun nuna cewa Gwamna Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP ya bai wa babban abokin hamayyarsa Ize Iyamu na jam'iyyar APC tazara da dubban ƙuri’u. I zuwa ƙarfe tara na safiyar ranar Lahadi, hukumar INEC a cibiyar tattara sakamakon zaɓe a Benin, babban birnin jihar Edo ta ce Obaseki na PDP ya samu ƙuri’u mafi rinjaye a ƙananan hukuma 11 a yayin da Ize Iyamu ya lashe zaɓe a ƙananan hukumomi biyu. Ga sakamakon zaɓen na ƙananan hukumomin: Karamar Hukumar EGOR APC: 10202 PDP: 27621 Karamar Hukumar OWAN EAST APC: 19295 PDP:14762 Karamar Hukumar OVIA NORTH EAST APC: 9,907 PDP: 16,987 Karamar Hukumar ETSAKO WEST APC: 26,140 PDP: 17,959 Karamar Hukumar ESAN WEST APC: 7,189 PDP: 17,434 Ƙaramar Hukumar ESAN SOUTH EAST APC: 9237 PDP: 10563 Ƙaramar Hukumar OREDO APC: 18365 PDP: 43498 Ƙaramar ...

KUKA NADA MATUƘAR AMFANI GA JIKIN ƊAN ADAM

Image
  AMFANIN MIYAR KUKA BBC hausa Kuka bishiya ce mai asali da ake samu a nahiyar Afirka da kuma wani yanki na kasashen Larabawa. A al'adance bishiyar kuka tana da matsayi da muhimmanci ga abinci da magungunan mutanen Afirka. Kuka tana kunshe da muhimman sinadarai masu gina jiki kuma masu inganta lafiya, kamar yadda mujallar lafiya ta Healthline ta bayyana a wani bincikenta game da amfanin kuka ga lafiyar dan Adam. Tun daga ganyen kuka da ɓawon da ƴaƴan kuka dukkaninsu suna da sinadarai masu amfani sosai a jikin mutum. Mujallar ta ce kuka tana ƙunshe da kusan dukkanin sinadaran da jikin mutum yake buƙata - Kuka na da sinadarin Calcium da ke taimakawa wajen ƙwarin kashi da hakori da sinadarin magnesium wanda yake daidaita jini. Kuka tana kuma da sinadarin iron wanda yake kare jiki daga kamuwa da cutar rashin jini, haka kuma kuka tana da sinadarin potasium da ke sasaita jini. Sannan uwa uba sinadarin Vitamin C ya fi yawa a kuka wanda ke yaƙi da cututtuka. Sauran sinadaran da ke cikin ku...

Amfara tattara sakamakon zaɓen jihar Edo

Image
  Tun ƙarfe 2:30 na rana kusan duka rufunan zaɓen da ke ƙananan hukumomi 18 na Edo suka rufe tantance masu zaɓe inda kuma wasu a lokacin suka fara ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa. Sai dai akwai wasu rumfunan zaɓen kayayyakin zaɓe ba su isa da wuri ba, wanda hakan ya sa ba su fara zaɓe da wuri ba. Tuni wasu rumfunan zaɓen suka ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa, inda Jam'iyyu biyu da suka fi shahara na APC da PDP ke nasara. A yanzu dai an fara kai akwatuna gAmfara tattara sakamakon zaɓen jihar Edoundumomi inda ake tattara alƙaluman zaɓe. Gwamnan jihar Godwin Obaseki ne ke takara ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, sai kuma Fasto Osagie Ize-Iyamu ƙarƙashin Jam'iyyar APC. Sakamakon farko-farko da ya fara fitowa ya nuna duka 'yan takarar sun lashe rumfunan zaɓensu.

PDP ce akan gaba a zaɓen jihar Edo.

Image
 Yanzu-Yanzu daga zaben Edo: Sakamakon farko ya nuna cewa dan takarar PDP, Gwamna Obaseki ne a gaba Rahotanni daga jihar Edo sun bayyana vewa sakamkon zaben gwamna dake gudana a jihar na farko ya bayyana kuma dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP,  Gwamna Godwin Obaseki ne akan gaba. Sakamkon wanda ya fito daga mazabar Ohe Ozua dake karamar hukumar Uhumwode ya nuna kamar haka: APC 65. PDP 95. LP-1

Ƴan daban PDP na barazana ga zaɓen jihar Edo- APC

Image
 Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta yi ikirarin cewa 'yan daba da ke yi wa jam'iyyar PDP aiki suna zuwa rumfunan zabe da ake tunanin APC za ta samu rinjaye sun fatattakar masu zabe da ma'aikatan INEC. A sanarwar da Kakakin yakin neman zaben gwamnan Edo na APC John Maiyaki ya fitar, ya lissafa wasu rumfunan zabe da ya yi ikirarin 'yan daban sun tafi sun tarwatsa masu zabe.

Osagie-Iyamu ne na jam'iyyar APC ya lashe rumfar zaɓen sa.

Image
  Ɗan takarar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu, shi na ya lashe rumfar zaɓensa, kamar yadda takwaransa na PDP Godwin Obaseki ya lashe tasa. Ize-Iyamu na Jam'iyyar APC ya samu ƙuri'u 292, sai kuma Obaseki na PDP ya samu ƙuri'u 21.

ILLAR SHAN PARACETAMAL BA BISA ƘA'IDA BA.

Image
 ILLAR SHAN PARACETAMOL BA BISA UMARNIN LIKITA BA Daga Ibrahim Y. Yusuf PARACETAMOL Wannan shahararren magani ne akasar mu wanda manya da yara, maza da mata, tsoffi da dattawa kowa yasan shi, kuma kowa yasan sunan. Kai intakaice muku ma duk chemist din da aka rasa wannan maganin toh ba chemist bane. Maganin yayi popular ba wanda bai bude ido dashi ba; sannan magani ne cikin rukunin OTC wato wadanda basa bukatar sahalewa ko ganin rubutun likita wato (prescription sheet) kafin abaiwa mutum shi. Ba irin Antibiotics, Anti hypertensive, antimalarial, anti motility ko anti histamine bane dake bukatar rubutun likita. Paracetamol akowacce irin kasa aduniya mutum na iya zuwa pharmacy stores asayar masa. Mutanen mu na amfani dashi wajen maganin ciwon jiki, ciwon kai, zazza6i, da kasala. TOH SAI DE MENENE AIKIN MAGANIN A ZAHIRANCE Paracetamol magani ne daga dangin ANALGESICS wato magani me rage zugi ko radadin ciwo. Aikinsa kenan karka dad'a karka rage. TOH AMMA YA MUTANEN MU KE AMFANI DASHI ...

HUKUNCIN KISA DA KOTUN MUSULINCI DAKE KANO TA YANKEMA WANI MATASHI SHARIF AMINU MI ZAI BIYO BAYA?

Image
 HUKUNCIN KISA DA ALKALIN KOTUN SHARI'AR MUSULINCI DA KE KANO YA YANKE MA WANI MATASHI SHARIF AMINU- Wace dama ta rage masa yanzu kafin wa'adin wata ɗaya.  Bayan da babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta yanke wa mawakin nan Aminu Yahaya Sharif hukuncin kisa kan laifin aikata sabo na zagin Manzon Allah SAW, mutane da dama za su so su san mene ne abu na gaba kan zartar da wannan hukunci. A cewar alkalin da ya yanke hukuncin Mai Shari'a Aliyu Mohammed Kani, mawaƙin yana da kwana 30 don daukaka kara. Me zai faru a Kotun Ɗaukaka Ƙarar? Barista Musa Salihu lauya ne a Abuja babban birnin kasar, ya ce abin da zai faru idan an je Kotun Daukaka Kara shi ne za a yi amfani da dokokin Najeriya ne ba na Shari'ar Musulunci ba. Ya ce: ''Idan Yahaya ya yanke shawarar daukaka kara, to zai samu sauki inda ba za a yi masa hukunci da Shari'ar Musulunci ba sai na dokokin Najeriya wadanda za su iya sauya hukuncin da Kotun Shari'a ta yanke masa.''  Wacce dama ta rage w...

ALLAH WADARAN NAKA YA LALACE

Image
 ALLAH WADARAN NAKA YA LALACE! Bayan fashewar da ta faru a Labanon, shin Amurka ta sauya matsayinta ne kan Labanon, daga matsin lamba zuwa ga 'taimako'? Toh alamu dai suna nuni da hakan. Babban dalili kuwa shi ne ziyarar da babban sakataren kungiyar kasashen larabawa Nabil al-Arabi ya kai kasar Labanon, bayan tsawon lokaci na fita sha'anin kasar, da kuma maganganu kan 'ba ta taimako don farfado da kasar' etc da yayi. Abin da ya sa na ce haka shi ne kuwa babu wani abin da za ka ga wadannan larabawan suna yinsa, mai kyau ne ko mara kyau, face sai da amincewar Amurka, kasar Siriya ta ishe mu misali. Don haka tun da na ga kungiyar kasashen larabawan ta shigo, to na san akwai "green light" daga Trump, wanda a halin yanzu ya ke neman duk wani abin da zai samar masa da komai kashin nasara  don ya yi amfani da shi wajen zabe, shi ya sa ma a halin yanzu Trump ya fara magana kan cimma yarjejeniya da Iran da Koriya ta arewa, kar ka sha mamaki ka ga wadannan kasashen ...

FASHEWAR SINADARAI A LABANON KO TARIHI ZAI MAIMAITA KANSA NE? daga Awwal Bauchi

Image
FASHEWAR SINADARAI A LABANON...KO TARIHI NA SHIRIN MAIMATA KANSA NE? A halin yanzu dai dukkanin idanuwa sun koma ƙasar Labanon sakamakon fashewar da ta faru a tashar bakin ruwa ta Beirut, babban birnin ƙasar, wacce ta yi sanadiyyar mutuwa da raunana daruruwan mutane. A daidai lokacin da ƙasashen duniya suke ta nuna alhininsu kan wannan lamari da kuma aikewa ko kuma alƙawarin aikewa da kayayyakin agaji, gwamnatin ƙasar dai ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar hakan da kuma alƙawarin hukunta duk waɗanda suke da hannu ciki, haka nan ƙungiyoyi daban-daban na ƙasar suna ci gaba da Allah wadai da faruwar hakan duk da cewa wasu kuma tamkar wata dama ce ta samu don cimma tsohuwar ‘baƙar’ aniyarsu a kan ƙasar. Tambayar da dai take yawo a halin yanzu ita ce shin ko tarihi ne ya ke ƙoƙarin maimaita kansa a Labanon ɗin? Shin waye zai amfana da wannan fashewar? Idan dai ana iya tunawa shekaru 15 da suka gabata ƙasar Labanon ɗin ta shiga shigen irin wannan yanayin, sa...