SHU'UMIN WURI A CIKIN TEKU MAI MATUƘAR HAƊARIN GASKE.
Bermuda Triangle: Shu'umin wuri mai hatsarin gaske da yake a cikin teku. 'Yan magana na cewa; "Rijiya gaba dubu,kin ci dubu sai ceto." To shi wannan wajen na Bermuda Triangle shu'umin wuri ne da yake a cikin Tekun Atalantika, wanda za a iya kiransa da cewa ya ci Miliyan dubu sau dubu sai ceto,duba da Karin maganar can ta 'yan magana. Wuri ne mai Siffar fili kusurwa Uku,mai Fadin murabbu'ai dubu goma a cikin Teku. Wurin yana shata wani ramin ruwa kamar bakin Rijiya. Wurin yana fizgo duk wani abu idan yai kuskuren gittawa ta daidai wajen;daga kasa ne,ko daga Sama. Wajen akwai karfin Maganadisu mai tsananin Karfin gaske wanda yake fizgowa da jawowar kowane abu kamar Kifi, Jirgin ruwa, jirgin Sama, Na'ura, koma dai menene muddin ya gitta ta wajen. Ruwan wannan waje ya kan tashi yayi tsiriri zuwa sama kuma duk abin da ya gitta ta wajen to fa shi tashi ta kare kenan har abada. Tun a shekarun 1900 aka gano shu'umcin wannan waje wanda...