Labari Maras Dadi: Wani Dan Bautar Kasa A Katsina Ya Yi Wa Yarinya 'Yar JSS1 Fyade.
Wani kwafa ya yi wa 'yar Karamar Sakandare JSS 1 fyade a Katsina. Wani matashi mai yi wa kasa hidima a Katsina, ya yi wa wata yarinya 'yar karama da ke aji daya na karamar sakandare wato JSS 1 fyade. A ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah, ya ce dalibar 'yar makarantar da kwafan ke yin hidimar kasarsa ne a ciki. A yanzun haka matashin da aka boye sunansa, na can garkame a caji ofis din 'yan sanda na Sabon-Garin, inda ake ci gaba da gudanar da bincike. Sai dai a bangaren mai magana da yawun hukumar matasa masu yi wa kasa hidima na jihar Katsina, Alex Oboaemeta, ya musanta zargin da ake yi wa memban nasu. inda ya ce ana jiran sakamakon binkice a kan fyaden. An dai ruwaito cewa yarinyar ta je dakin mai yi wa kasa hidimar ne da ke cikin makarantar, inda a nan ne ya lalata mata rayuwa. Ko mi albarkacin bakinku zai fadi akan haka?