Halin da ƙasa take ciki- wasu jigajigai a APC sun bada hakuri.
Wasu jigajigan jam'iyyar APC mai mulki sun fara neman afuwar jama'ar Nigeriya. Wasu jiga-jigan 'yan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun fara neman afuwar 'yan kasar a kan da su yi hakuri dangane da yanayin kunci da kasar take ciki yanzu haka sakamakon wasu matakai da gwamnatin kasar ke dauka da manufar gyara. Daya daga cikin jigo a jam'iyyar Farouk Adamu Aliyu, a cikin wata hira da ya yi da BBC, ya ce jama'a su yi hakuri da halin da ake ciki na matsi wanda ya ce dalilai ne suka haddasa hakan. Farouk Adamu Aliyu ya ce:"Ni ma a iya sanina ba na zaton an taba shiga kunci irin wannan na yanzu, kamar a bangaren abinci gaskiya ne an samu matsalar hauhawar farashi da dai sauransu". Ya ce abubuwa da dama ne suka kawo hakan, yana mai cewa mutane da dama sun sha kiransa ana yi masa Allah ya isa saboda yadda rayuwa ta yi kunci a yanzu. Jigo a jam'iyyar ta APC ya c:" Ga wadanda suke da-na- sanin tallafa mana da wani abu a lokacin da muke yakin ne...