ASALIN CUTAR CORONA VIRUS DA KUMA YANDA ZA'A KAUCE MATA
Hanyoyin Riga-Kafin Kamuwa Da Cutar Koronabairus Daga Dakta Shu’aibu Musa Cutar Koronabairus wani nau’in cuta ne da kwayoyin cuta da bairus ke kawowa dangin kwayoyin cuta da ke janyo cutar mura ko mashako da wasu cututtuka masu tsanani. COVID-19 shi ne sunan da aka sa wa sabuwar kwayar cutar da ke janyo cutar Korona da ta zama annoba. A yanzu tana neman ta mamaye duniya. An fara gano wannan kwayar cutar ne a 2019 a yankin Wuhan na kasar Sin (China). Cutar Korona, cututtuka ne da ake dauka daga dabbobi. A can baya an yi wasu nau’o’in cututuka da Korona bairus ke kawowa, kamar cutar murar tsuntsaye da ake dauka daga tsuntsaye da cutar haukan shanu da sauransu. Akwai ma cututtuka da dama da Korona bairus ke kawowa da ke shafar dabbobi ne kawai, amma ba su riga sun fara shafar mutane ba. Manyan alamomin wannan ciwon Korona din sun hada da:- Zazzabi da tari da numfashi sama-sama, ko daukewar numfashi. In cutar ta tsananta, takan zamanto tamkar ciwon ‘pneumonia’ (nimoniya), ko ciwon ...