Posts

YANDA AKA KAMA ƊAN CIA JAMSHID SHARMAHD-

Image
Nasir Isa Ali - Jamshid Sharmahd (Dan CIA) Ya bar jihar California inda yake zaune, kuma daga nan yake jagorantar kungiyarsa ta 'Thunder' zuwa Dubai domin haduwa da abokan kasuwancinsa. Daga nan bamu kara jin duriyar wayarsa ba,sai daga baya. Amma bayanan farko sun nuna cewar,an bibiyi wayar tasa ta hanyar wani tauraron dan adam,sai aka gano cewar,daga Dubai aka tsallaka da shi zuwa kasar Oman,kana aka bi ta hanyar ruwa zuwa Iran da shi. - Mu mun san cewar Sharmahd ya tsara cewar,daga Dubai zai wuce zuwa kasar India ne domin yin cininkin kayayyakin kamfaninsa na komfuta. Lokacin da aka fada mana cewar an shigar da shi cikin wata mota mai duhu kuma an tsallaka da shi zuwa Oman sai hankalin mu ya tashi sosai. Sai daga baya muka gan shi an daure masa fuska da bakin kyalle ana nuna shi kan talbijin din Iran cewar 'jami'an leken asirin Iran sun yi Ram da shi. - Lallai baban namu ya bugo mana waya daga wani hotel dake cikin filin saukar jiragen sama na Dubai,kana yace mana ya...

ABIN LURA: game da yaƙi da CORONAVIRUS

Image
Abin lura game da yaki da cutar Corona Virus Daga Abdulmumin Giwa Da farko zan ba da hakurin yin rubutun da ingausa. Problem din shine babu test kits da za a gwada mutane a kare rayuwarsu. Na ji an ce an samu gwada kimani mutane 700 kacal a Nigeria daga cikin mutane miliyan 200. Akwai tsarin kiwon lafiya da ake cewa Preventive Healthcare sannan kuma akwai Curative healthcare. Shi Preventive Healthcare aikin lafiya ne na kariya daga kamuwa da ga cuta. Za a kareka daga kamuwa da shi ta hanyoyin aikin lafiya daban daban. In an lura za a ga cewa gwamnati ba ta komai a wannan sashi game da wannan annoba ta Corona Virus. Kamata ya yi ana gwada mutane ana kebe wadanda aka samu don warkar dasu kafin ya tumbatsa. Kuma kamata ya yi a rika feshi a wuraren jama'a kamar kasuwanni, wuraren ibada, malls, unguwanni da sauransu. Amma ba a komai ta wannan fannin. A daya hannun kuma, shi Curative Healthcare tsarin lafiya ne ba warkar da wanda ya kamu da cuta. Wannan bangaren shine gwamnati ...

TSAWA DA RUGUGI A BIRNIN RIYADH

Image
Nasir Isa Ali Mazauna birnin Riyadh sun shiga zaman zullumi bayan sun ji kara da rugugin fashewar wani abun fashewa. - Bayan rundunar tsaron birnin Riyadh ta bayyana cewar,ta samu sa'ar kado wani makami mai linzami wanda yan Huthy suka harbo kan birnin a cikin daren lahadi,sai ga wata kara da rugugi ya afku kan birnin na Riyadh. Gidan TV din Al-Arabiyya ya bayyana cewar, rundunar tsaron Samaniyar Saudiya sun karkado wasu makamai biyu wanda aka harbo daga Yemen zuwa kan Riyadh da Jizan. Haka zalika tashar El-Akhbariyya ta bayyana cewar, rundunar tsaron Saudiya sun kado wani makami mai cin nisan zango (Ballistic-Missile) a sararin samaniyar birnin Riyadh. - Amma kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewar,wakilansa sun jiyo wasu karar farfashewa da rugugi mai karfi a birnin na Riyadh. Su ma kansu mazauna birnin na Riyadh sun bayyana cewar sun jiyo kara da fashewar wasu abubuwa,tare da jin rugugi,daga baya kuma suka jiyo jiniya ! Alamar kowa ya zauna a inda yake. - Har yan...

CORONAVIRUS: Allah buwayi gagara misali.

Image
COVID-19: KARFIN MULKIN ALLAH YA KARA BAYYANA A ZAHIRI... A yanzu kasa mafi karfin soja a Duniya, tare da karfin tattalin arziki, wacce take ganin kamar ta gagari komai da kowa, ta zama abar tausayi, ta rikice tana ta neman tallafi daga ko ina sakamakon annoba guda daya kacal data ziyarcesu, Yau dukkan manya manyan Hotels dake Las Vegas sun kasance a kulle, guraren Chacha dake les Vegas suna kulle, layukan dake kasar Amsterdam inda ake gudanar da karuwanci mafi tsada a duniya duk an rufesu, duk da makudan kudaden da ake samu har sama da 10 Billion Dollars a shekara, an wayi gari a duniya kowacce kasa ta rufe Night Clubs da guraren shan giya tare da guraren da ake taruwa domin aikata masha'a lallai Allah da karfi yake... Da karfin ikon Allah yau kusan dukkan jiragen sama suna kasa a ajiye, an dena amfani dasu sakamakon tsoron annobar Coronavirus, shi kansa Shugaba Trump na amurka da bakinsa yake bayyana cewa kasarsa zata dakatar da karbar kudin ruwa don a samu sauki a halin da...

ASALIN CUTAR CORONA VIRUS DA KUMA YANDA ZA'A KAUCE MATA

Image
Hanyoyin Riga-Kafin Kamuwa Da Cutar Koronabairus Daga Dakta Shu’aibu Musa Cutar Koronabairus wani nau’in cuta ne da kwayoyin cuta da bairus ke kawowa dangin kwayoyin cuta da ke janyo cutar mura ko mashako da wasu cututtuka masu tsanani. COVID-19 shi ne sunan da aka sa wa sabuwar kwayar cutar da ke janyo cutar Korona da ta zama annoba. A yanzu tana neman ta mamaye duniya. An fara gano wannan kwayar cutar ne a 2019 a yankin Wuhan na kasar Sin (China). Cutar Korona, cututtuka ne da ake dauka daga dabbobi. A can baya an yi wasu nau’o’in cututuka da Korona bairus ke kawowa, kamar cutar murar tsuntsaye da ake dauka daga tsuntsaye da cutar haukan shanu da sauransu. Akwai ma cututtuka da dama da Korona bairus ke kawowa da ke shafar dabbobi ne kawai, amma ba su riga sun fara shafar mutane ba. Manyan alamomin wannan ciwon Korona din sun hada da:- Zazzabi da tari da numfashi sama-sama, ko daukewar numfashi. In cutar ta tsananta, takan zamanto tamkar ciwon ‘pneumonia’ (nimoniya), ko ciwon ...

Tsohon Shugaban Kasa Abdussalam Abubukar Ya Zargi Shugaba Buhari Da Rashin Aiki Da Rahotonsu Kafin A Tsige Sanusi.

Image
Tsige Sarkin Kano: "Da Buhari Yayi Amfani Da Rahotonmu da Ba A Tsige Sarki Sunusi ba" -Gen. Abdussalamu Abubakar. Tsohon shugaban Kasa kuma shugaban kwamitin sasanta tsohon Sarkin Kano Sanusi da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje, Abdussalami Abubakar ya bayyana cewa lallai da a ce Buhari ya duba shawarwarin da suka bada a rahoton su da yana ganin ba zai kai ga tsige sarki Sanusi ba. Abdussalami Abubakar ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a hira da yayi da muryar Amurka. "Babban abin da ya bani mamaki shine yadda abin ya kai ga har an tsige sarki Sanusi. "Lallai mun zauna da Sarki Sanusi daban kuma mun ji daga garesa,sannan mun zauna da Gwamna Abdullahi Ganduje,shi ma mun tattauna da shi matuka.Bayan haka mun bar su tare sun zauna sun tattauna kafin nan muka rubuta sakamakon ganawar mu da su. "Abin da muka ji sannan muka gani, ban yi tunanin har zai kai ga wannan matsayi da mukashiga yanzu ba. Bayan mun Kammala zaman mu da su, m...

Cutar Corovirus A Iran: "Damuwa Da Talakawan Kasarsu Da Jami'an Gwamnatin Kasar ta Iran Ke Yi Yasa Manyan Jami'an Gwamnatin Kasar Suka Fi Kamuwa da cutar Coronavirus" -Inji Daraktan WHO

Image
An Bayyana Dalilan Da Yasa Manyan Jami'an Gwamnatin Kasar Iran Ke Kamuwa Da Cutar CoronVirus. Daraktar kungiyar lafiya ta duniya (WHO) a gabashin duniya Dr.Rechard Brennan ya bayyana dalilan da yasa manyan Jami'an gwamnatin Kasar Iran ke kamuwa da cutar shake makoshi na Korona Bairus(COVID-19. Daraktan ya bayyana hakan ne a birnin Tehran a lokacin da ya ziyarci Iran,kana ya ziyarci inda ake killace da masu cutar domin ya gane wa idonsa yadda ake kula da lafiyarsu. inda ya yi kira ga kasashen duniya da su yi koyi da kasar ta Iran wajen yakar cutar wannan cuta ta Korona. Dr.Rechard ya kuma bayyana cewar,Iran ta ciri tuta wajen yin yaki da wannan cutar, sannan yayi kira ga kasashen yankin da duniya baki daya da su yi koyi da Iran wajen yakar wannan cutar. Ya kara da cewar,Iran tana da ingantattun kayan aiki na zamani masu kyawun gaske,kuma a yankin Asiya kakaf bai ga kayan aiki irin na Iran din ba. Yace kungiyarsa ta WHO ta bada sharuddan yakar wannan cutar,kuma Iran ...

Saudiyya: Yarima Bin Salman Na Tsaka Mai Wuya.

Image
Rikici A Saudiyya: Ana Zargin Yarima Muhammad Bin Salma da Kame-Kamen 'Yaya Da Jikokin Manya A Masarautar Saudiyya. Rikici tsakanin 'yaya da jikokin Ahli Sa'ud yana ta kara kamari a masarautar a 'yan kwanakin nan inda Rundunar kare masarautar Saudiyar ta kara cafke wasu 'yayan gidan su Uku ciki kuwa har da wasu manyan yarimomi biyu. Rahotannin da ke fitowa daga masarautar na tabbatar da cewar,da sanyin safiyar yau Asabar ne aka cafke Yarima Ahmad bin Abdulazee shakikin sarkin Saudiya na yanzu (Salman bin Abdulazeez) da kuma yarima Muhammad bin Nayef kamar yadda mujallar "Wall Street Journal" ta ruwaito. Ana kyautata zaton cewar,ayyanannen yariman Saudiya Muhammad bin Salman da mahaifinsa suna da hannu dumu-dumu wajen wannan kitimurmura ta Kamesu. Jaridar "The New York Times" ta habarto labarin kuma ta kara da cewar,ita ma ta samu rahoton cewar,an kama dan uwan yarima Nayif wato Nawaf bin Nayef. Ya kawowa yanzu dai, hukumomi a masaraut...

Maganin Korona Bairus A Iran: Kasashe Na Ta Rokon Iran Da Ta Taimaka Masu Da Shi.

Image
Bayan fitar a rahoton kungiyar lafiya ta duniya (WHO) kan Iran,abokan aikin ministan harkokin kasashen wajen Iran,Muhammad Jawad Zarif sun yi ta bugo masa waya domin neman hadin kan Iran kan yakar cutar Corona bairus,tare da jinjina wa Iran din. Da farko ministan harkokin wajen kasar Norway Mr.Marie Eriksen Sorede ne ya bugo waya, yana mai tunatar da Zarif din game da yarjejeniya Oslo wanda Iran da kasar suka sanya wa hannu cewar za su hada kai wajen taimakawa junansu kan lamurra daban-daban,ciki kuwa har da sha'anin kiwon lafiya. Daga nan kuma sai na kasar Switzerland Mr,Ignazio Cassis ya bugo waya yana mai tambayar halin da ake ciki a Iran din game da cutar ta Corona. Sannan suka tattauna yadda sauran kasashen duniya ke ciki game da cutar,da kuma matakan ci gaban da ita Iran din ta samu wajen yakar cutar. Daga nan kuma ministan harkokin wajen kasar Austria Mr.Alexander Schallenberg ya bugo waya yana taya Iran murnan samun cigaba wajen yakar wannan cutar,tare da kira ga Ir...

Matsalar Tsaro a Najeriya: Shaikh Bala Lau Ya Yi Kira Da A Koma Ga Allah Kurum.

Image
"Komawa Zuwa ga Allah Shi ne Maganin Fitinun Ƙasar Nijeriya" – Sheikh Bala Lau. Shugaban ƙungiyar IZALA na tarayyar Nijeriya, Ash-Sheikh Dr Imam Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa komawa ga Allah Maɗaukakin Sarki ne maganin fitintinu da suka addabi ƙasar Nijeriya. Sheik Bala Lau ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da 'yan jarida a gidan sa dake Yola. Bala Lau yace a duk lokacin da annoba, ko bala'i ya samu mutum, to abu na farko shine ya komawa Allah. Yace dole ne sai mutane sun fahimci cewa babu mutum da zai iya yaye fitina ko bala'i idan ya taso wa al' umma face Allah. "Idan ka dauki kasar nan tun daga zamanin su Sardauna, wadanda suka san tarihi sun san irin matsaloli da su sardauna suka fiskanta duk da ƙoƙarin su da adalcin su mutane a wancan lokacin suna gani tamkar sun kasa, wanda hakan ne ya haifar da rayuwar su ta tafi ta wannan hanya "Saboda haka, kowani zamani da irin jarrabawa da mutane suke fiskanta, daga zamanin '...

Labari Maras Dadi: Wani Dan Bautar Kasa A Katsina Ya Yi Wa Yarinya 'Yar JSS1 Fyade.

Image
Wani kwafa ya yi wa 'yar Karamar Sakandare JSS 1 fyade a  Katsina. Wani matashi mai yi wa kasa hidima a Katsina, ya yi wa wata yarinya 'yar karama da ke aji daya na karamar sakandare wato JSS 1 fyade. A ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah, ya ce dalibar 'yar makarantar da kwafan ke yin hidimar kasarsa ne a ciki. A yanzun haka matashin da aka boye sunansa, na can garkame a caji ofis din 'yan sanda na Sabon-Garin, inda ake ci gaba da gudanar da bincike. Sai dai a bangaren mai magana da yawun hukumar matasa masu yi wa kasa hidima na jihar Katsina, Alex Oboaemeta, ya musanta zargin da ake yi wa memban nasu. inda ya ce ana jiran sakamakon binkice a kan fyaden. An dai ruwaito cewa yarinyar ta je dakin mai yi wa kasa hidimar ne da ke cikin makarantar, inda a nan ne ya lalata mata rayuwa. Ko mi albarkacin bakinku zai fadi akan haka?

Ta Yafe Mai Sadakinta Bayan Ya Yi Mata Alkawalin Ba Zai Yi Mata Kishiya Ba Har Abada.

Image
Alkawalin Cewa Ba Zai Yi Wa Amaryarsa Kishiya Ba,Ya Ja Masa Tagomashin Yafe Sadakin Aurensa Daga Matar Da Zai Aura. Wata amarya Ta Yafe Wa Ango Sadakinta, bayan angon ya yi alkawarin ba zai yi mata kishiya ba har su kwanta daka. Wata mata mai suna Aishat Busari ta wallafo cewa, wata amarya ta ce ta yafe sadakin aurenta ga angonta,amma sai dai ta ce angon ya yi mata alkawari a bainar jama’a cewa ba zai yi mata kishiya ba.  Wannan dai ya faru a Offa, jihar Kwara, inda amaryar mai suna Fatima Babawale ta ce ta yafe sadakinta a daurin aurenta da aka yi ranar 15 ga watan Fabrairun 2020. A musulunce sadaki na daya daga cikin sharuddan aure, amma ya danganta da yarjejeniyar ango da amarya a kan abin da za a bayar a matsayin sadakin auren. Yadda abin ya faru shi ne; a lokacin daurin auren Muhammad Adebayo da Fatima Babawale, ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu, 2020, Alfa ya bukaci Muhammad ya fito ya biya sadaki, sannan kuma ya tambayeshi wane irin sadaki zai bayar, Muhammad na sh...

HIZBULLAH NA SHIRIN TSAYAR DA AL'ƘIYAMAR ISRA'ILA- Dattijan Yahudawa sunyi Gargadi

Image
Hezbolla Da Isra'ila: 'Hezbolla na shirin tsayar da Alkiyamar Israila' -Dattawan Yahudawa Sun gargadi Netanyahu. Wasu dattawan Yahudawa,Sojoji da 'yan Siyasa,sun bayyana cewa Hezbollah fa na shirin tsayar da Alkiyamar Isra'ila muddin Netanyahu ya takulo yaki da Hezbollah. Yahudawan su bayyana wa kafofin sadarwar Israila cewar,duk wani yaki da Hezbollah a nan gaba to zai zamo tamkar tashin alkiyama ne ga Isra'ila. Da farko, tsohon Firayemiyar Israila Mr.Ehud Barak ya bayyana cewar,Hezbollah ta mallaki makami mai linzami mai cin dogon zango,wanda kuma ake iya sarrafa shi da na'ura daga nesa 'Precision-Guided Missile (PGM). Mr.Ehud Barak ya bayyana cewar,akwai wurare muhimman gaske wanda Hezbollah za su hara idan yaki ya barke tsakaninsu da Israila. Ya ce za su hari a gine-ginen gwamnati da wasu muhimman wurare kamar ma'aikatar tsaron Israila. Ya bayyana cewar,hatta ofishin Firayeministan Israila da ginin majalisar kasar (Knesset) ba fa za s...

SHU'UMIN WURI A CIKIN TEKU MAI MATUƘAR HAƊARIN GASKE.

Image
Bermuda Triangle: Shu'umin wuri mai hatsarin gaske da yake a cikin teku. 'Yan magana na cewa; "Rijiya gaba dubu,kin ci dubu sai ceto." To shi wannan wajen na Bermuda Triangle shu'umin wuri ne da yake a cikin Tekun Atalantika, wanda za a iya kiransa da cewa ya ci Miliyan dubu sau dubu sai ceto,duba da Karin maganar can ta 'yan magana. Wuri ne mai Siffar fili kusurwa Uku,mai Fadin murabbu'ai dubu goma a cikin Teku. Wurin yana shata wani ramin ruwa kamar bakin Rijiya. Wurin yana fizgo duk wani abu idan yai kuskuren gittawa ta daidai wajen;daga kasa ne,ko daga Sama. Wajen akwai karfin Maganadisu mai tsananin Karfin gaske wanda yake fizgowa da jawowar kowane abu kamar Kifi, Jirgin ruwa, jirgin Sama, Na'ura, koma dai menene muddin ya gitta ta wajen. Ruwan wannan waje ya kan tashi yayi tsiriri zuwa sama kuma duk abin     da ya gitta ta wajen to fa shi tashi ta kare kenan har abada. Tun a shekarun 1900 aka gano shu'umcin wannan waje wanda...

Wata Budurwa Ta Shirya Za6en Wanda Za Ta Aura Tsakaninta Samarinta A Bauchi.

Image
Khadija: Budurwar Da Ta Shirya zaben Fidda Gwanin Da Za Ta Aura A Tsakanin Samarinta. Wani abu kamar al'amara da ya faru a Karamar hukumar Giade ta Jihar Bauchin Tarayyar Najeriya,wata Budurwa ta shirya wa Samarinta biyu Za6en fidda gwani da zummar auren duk wanda ya lashe Za6en.  Budurwar mai suna Khadija tana da samari biyu; Inusa da Ibrahim dukkansu suna neman aurenta ita ma tana sonsu,amma sai dai ta kasa za6en daya Tilo bisa ra'ayinta domin ta aura, sakamakon yadda kwarjininsu ya dabaibayeta har sai da ta kai ga shirya za6en fidda gwani a tsakaninsu,za6en da Jama'ar kowanensu suka gabatar. Bayan samarin sun yi yawon Campaigh(yakin neman za6e) a cikin maza6arsa,sai aka shirya za6e inda magoya bayan kowanensu ya bi layi ya kada Kuri'arsa,za6en wanda Manyan anguwa suka yi alkalancinsa. Bayan tattara sakamakon za6e,an bayyana Inusa a matsayin wanda ya lashe za6en inda abokin hamayyarsa Ibrahim ya sha kaye ya kuma rungumi kaddara. Tuni dai an ba wa Inusa '...

Iran Ta Yi Bikin Tunawa Da Zagayowar Ranar Samun 'Yancin Kai.

Image
An Yi Bikin Tunawa Da Zagayowar Ranar Yuyin Juya-Hali Karo Na 41 A Kasar Iran. Daga Auwal Isa Musa. Magoya bayan kare Juyin-juya halin kasar Iran a jiya Talata,sun fito kwansu da kwalkwatansu domin jaddada mubayi'arsu ga tsarin da Kasar ke tafiya akanshi na Musulunci. Hakan na zuwa ne a lokacin da Kasar ta Iran ke bikin cika shekaru 41 cur da samun 'yancin kai na Juyin-juya hali daga Mulkin gurguzu zuwa na Musulunci da Malamin Addini Ayatollahi Ruhulla Alkhomaini ya Jagoranta a shekarar 1979. Duk ranar 11 ga Fabrelun kowace shekara dai, Al'ummar Kasar ta Iran na yin fitar farun-dango domin nuna farin cikinsu da yi wa juna barka gami da yin godiya ga Allah akan wannan sauyi da suka samu sama da shekaru 40,inda su kan gudanar da abubuwa daban-daban a matsayin shagulgula. Babban abin da Al'ummar kasar ke yi a wannan rana shi ne Muzaharori(demonstrations) a inda suke tafe suna rera wakokin Murna tare da daga Hotunan Jagoran wannan sauyin wato Ayatollah Alkhomaini,...

Dubun Wata Shedaniyar Dorinar Ruwa Ya Cika Jihar Kebbi.

Image
Dubun Wata Dorinar Ruwa Ya Cika A Jihar Kebbi. Daga Wakilinmu. Dubun wata dorinar ruwar da ta dade tana yin 6arna a garin sa-ma-na-ji da ke karamar hukumar Koko/Bessen jihar Kebbi ya cika,inda Mutanen garin suka yi nasarar zakulota a cikin ruwa suka kuma hallata barzahu. Kafin samun nasarar kashe wannan Dabbar ruwan,kamar yadda rahotanni suka bayyana,ta dade tana yi wa al'ummar wannan gari mummunar 6arna ta hanyar hallaka masu Dabbobi,lalata gonaki har ma da salwantar masu da rayukan jama'a,inda daga karshe dai mutanen yankin suka fusata suka yi wa kududdufin da take ciki kawanya suka kuma hallakata har lahira bayan shafe tsawon yini guda cur suna artabu da ita. Barnar da aka tabbatar Dorinar ruwan ta ta6a yi wa mutanen garin ya hada da; nitsar da jirgin ruwa har sau hudu,lalata gonakin shinkafa har ma da rasa rayukan mutane. Jim kadan da samun wannan nasara ta kashe wannan dabbar ruwan,shugaban karamar hukumar Koko/Besse, Honarabul Yahaya Bello Koko,mataimakinsa Hona...

Kasar Iran Za Ta Halba Wasu Taurarin Dan Adam Masu Nisan Kilomita 1000 Daga Doran Kasa.

Image
Iran Za Ta Harba Taurarin Dan Adam Tsawon Kilo Mita 1000 Daga Doron Kasa. Shugaban hukumar kula da ayyukan sararin samaniya na kasar Iran, Mortadha Barari ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu masu zuwa Iran za ta harba wasu taurarin dan adam zuwa sararin samaniya tsawon kilo mita 1000 daga doron kasa. A lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Tehran, Barari ya bayyana cewa, baya ga shirin da suke dashi na harba wasu taurarin dan adam a cikin wannan makon mai kamawa, suna da wani shirin na daban tsakanin shekara guda zuwa shekaru biyu masu zuwa. Ya bayyana cewa wannan yana daga cikin babban ci gaban da suka samu a bangaren ilimin kimiyya, wanda ya mayar da Iran din ta zama ta daya ayankin gabas ta tsakiya wajen harba tauraron dan adam, kamar yadda kuma ita ce ta tara a duniya a halin yanzu a wannan fage. Ya ce kammala aikin shekaru biyu masu zuwa, Iran din za ta harba wasu taurarin dan adam tsawon kilo mita dubu 36 daga doron kasa.

Gwamna Zulum ya nuna rashin sha'awarsa na wani ya yi masa tattakin karramawa.

Image
'Ka sha zamanka ka huta na gode da kauna'- Sakon Gwamna Zulum ga matashi da ya fara tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri. Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira ga matashi Usman Zubairu, wanda ya sanar da cewa zai yi tattaki daga jahar Jigawa zuwa Maiduguri domin jinjinawa gwamnan kan ayyukan da yake yi cewa yayi zamansa amma ya gode. Gwamnan ya bayyana hakan ne da yammacin Juma'a a shafinsa na Tuwita Yace: "A'a, Nagode, dan uwa Usman Zubairu." Ya kara da cewa; "Na samu wani labarin cewa wani matashin dan uwa Usman Zubairu, ya kaddamar da tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri domin karramani." Ya ci gaba da cewa "Ina mai matukar godiya Malam Usman bisa ga goyon bayarka amma ina rokonka ya ajiye wannan tafiya." "A nawa fahimtar, ya zo Maiduguri tuni. Ina kira garemu mu sanya jihar Borno da Najeriya cikin addu'o'inmu. Hakan ya fi kyau." Usman Zubairu dai ya bayyana cewa zai yi tattaki daga jihar...

Batanci Ga Alzakzaky Ya Ja Wa Wani Matashi Hukunci A Kotu.

Image
Wata Kotu ta daure wani Matashin akan ya yi 6atanci da Hoton Shaikh Alzakzaky. A ranar talatar na da ta gabata (4/2/2020) ne, wata Kotun Majistare da ke Potiskum jihar Yobe ta yanke wa wani matashi mai suna Mohamad Garba hukuncin daurin watanni shida a gidan kaso ko kuma tarar Naira dubu 10,000 a bisa samunsa da laifin 6ata sunan Malamin Addinin Musulunci shugaban 'yan uwa Musulmi a Najeriya, Shaikh Alzakzaky,ta hanyar amfani da Hoton Malamin a cikin wani bidiyon 6atanci da ya yi wa wasu Mata ya sakie shi a kafafen sadarwa. Bidiyon mai tsawon mintuna biyu da dakika 40 da Matashin ya saki kafafen sadarwa na zamani a ranar 26 ga Janairun 2020,ya nuna yadda yake 6atanci ga wasu matan da ba su da Hijabi a jikinsu yana kuma tallatasu da cewa "ana gwanjonsu",a inda daga karshen bidiyon ya dauka da Hoton Malam Alzakzaky, sakamakn haka Almajiran Malamin suka yi kararsa da sunan ya yi 6atanci da zub da Mutunci wa Malamin nasu. Almajiran Malamin sun binciko matashin sukakuma ...