HUKUNCIN KISA DA KOTUN MUSULINCI DAKE KANO TA YANKEMA WANI MATASHI SHARIF AMINU MI ZAI BIYO BAYA?
HUKUNCIN KISA DA ALKALIN KOTUN SHARI'AR MUSULINCI DA KE KANO YA YANKE MA WANI MATASHI SHARIF AMINU- Wace dama ta rage masa yanzu kafin wa'adin wata ɗaya. Bayan da babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta yanke wa mawakin nan Aminu Yahaya Sharif hukuncin kisa kan laifin aikata sabo na zagin Manzon Allah SAW, mutane da dama za su so su san mene ne abu na gaba kan zartar da wannan hukunci. A cewar alkalin da ya yanke hukuncin Mai Shari'a Aliyu Mohammed Kani, mawaƙin yana da kwana 30 don daukaka kara. Me zai faru a Kotun Ɗaukaka Ƙarar? Barista Musa Salihu lauya ne a Abuja babban birnin kasar, ya ce abin da zai faru idan an je Kotun Daukaka Kara shi ne za a yi amfani da dokokin Najeriya ne ba na Shari'ar Musulunci ba. Ya ce: ''Idan Yahaya ya yanke shawarar daukaka kara, to zai samu sauki inda ba za a yi masa hukunci da Shari'ar Musulunci ba sai na dokokin Najeriya wadanda za su iya sauya hukuncin da Kotun Shari'a ta yanke masa.'' Wacce dama ta rage w...