FASHEWAR SINADARAI A LABANON KO TARIHI ZAI MAIMAITA KANSA NE? daga Awwal Bauchi
FASHEWAR SINADARAI A LABANON...KO TARIHI NA SHIRIN MAIMATA KANSA NE? A halin yanzu dai dukkanin idanuwa sun koma ƙasar Labanon sakamakon fashewar da ta faru a tashar bakin ruwa ta Beirut, babban birnin ƙasar, wacce ta yi sanadiyyar mutuwa da raunana daruruwan mutane. A daidai lokacin da ƙasashen duniya suke ta nuna alhininsu kan wannan lamari da kuma aikewa ko kuma alƙawarin aikewa da kayayyakin agaji, gwamnatin ƙasar dai ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar hakan da kuma alƙawarin hukunta duk waɗanda suke da hannu ciki, haka nan ƙungiyoyi daban-daban na ƙasar suna ci gaba da Allah wadai da faruwar hakan duk da cewa wasu kuma tamkar wata dama ce ta samu don cimma tsohuwar ‘baƙar’ aniyarsu a kan ƙasar. Tambayar da dai take yawo a halin yanzu ita ce shin ko tarihi ne ya ke ƙoƙarin maimaita kansa a Labanon ɗin? Shin waye zai amfana da wannan fashewar? Idan dai ana iya tunawa shekaru 15 da suka gabata ƙasar Labanon ɗin ta shiga shigen irin wannan yanayin, sa...